Amurka Nijeriya Siyasa Tsaro

Shin Matsin Lambar Amurka Na Iya Zama Dalilin Tsananta Rashin Tsaro a Najeriya?

Masu sharhi na ganin cewa irin waɗannan hare-hare na kara nuna yadda rashin tsaro ke ta’azzara, lamarin da ya sa ake tambayar ko akwai tasirin matsin lambar siyasa daga ƙasashen waje a cikin lamarin.

Newstimehub

Newstimehub

3 Dec, 2025

89fa1738 5d9b 4698 90bd ee39438f12fa.jpg e1764769608837

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana dokar ta-ɓaci a kan matsalar tsaro a ƙasar, tare da umartar jami’an tsaro su dauki matakan gaggawa, bayan sace sama da ɗalibai 300 a hare-haren ƴan bindiga da suka tsananta a arewa maso yammacin ƙasar cikin watan Nuwamba. Mummunan harin da ya fi daukar hankali shi ne wanda aka kai a ranar 21 ga Nuwamba a makarantar St. Mary’s Catholic School a jihar Neja, inda aka yi garkuwa da ɗalibai da malamai kusan 300. Rahotanni sun ce akalla mutum 50 sun kuɓuta, amma sauran suna hannun masu garkuwa da mutane har yanzu.

Kwana huɗu kafin haka, wasu ƴan bindiga sun sace ƙananan yara mata 25 daga makarantar gwamnati a ƙaramar hukumar Danko Wasagu, jihar Kebbi. Rahotanni sun tabbatar da cewa ɗalibai biyu sun tsere, sannan aka sake sauran 23 a ranar 25 ga Nuwamba bayan tattaunawar da gwamnati ta yi da masu garkuwa da mutanen.