Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 na naira tiriliyan 58.47 a gaban Majalisar Dokoki a ranar Juma’a. Kasafin ya mayar da hankali ne kan fannonin tsaro, ilimi da lafiya, waɗanda gwamnati ta ce su ne ginshiƙan ci gaban ƙasa.
A cikin kasafin, an ware naira tiriliyan 15.25 domin ayyukan yau da kullum na gwamnati, yayin da aka tanadi naira tiriliyan 26.08 don manyan ayyukan raya ƙasa da ababen more rayuwa. Kasafin ya kuma dogara da hasashen farashin gangar ɗanyen mai a dala 64.85 da kuma samar da ganga miliyan 1.84 a rana, tare da ƙididdigar canjin dala kan naira 1,400.
Fannin tsaro ne ya fi samun kaso mafi yawa, inda aka ware masa naira tiriliyan 5.41, sai aikace-aikace da kimiyya da ilimi da suka samu kaso mai tsoka. Gwamnatin ta bayyana fatan cewa kasafin zai taimaka wajen farfado da tattalin arziki, rage talauci da samar da ayyukan yi, duk da ƙalubalen hauhawar farashi da rashin aikin yi da ƙasar ke fuskanta.
Majiyar labari: Trt hausa














