A safiyar Litinin ne aka ga sojojin Sudan suna shiga birnin Dilling a jihar Kudancin Kordofan cikin murna, bayan sun karya ƙawanyar da mayaƙan RSF suka yi wa birnin na tsawon sama da shekara ɗaya da rabi, lamarin da ya sa mazauna yankin suka yi wa dakarun maraba a yayin da suka rika zagaya cikin manyan motocin yaki.
Rundunar sojin ta bayyana cewa ta buɗe hanyar shiga birnin ne bayan gagarumin farmaki da ya jawo mummunar asara ga RSF, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da yaƙi har sai an maido da zaman lafiya a faɗin ƙasar. Dilling na da muhimmiyar matsayi domin yana kan hanyar zuwa Kadugli da El-Obeid, manyan biranen da ke cikin barazanar ƙawanya.
Farmakin ya zo ne a daidai lokacin da RSF ke ƙoƙarin faɗaɗa ikonta a yankin Kordofan, bayan ƙwace Heglig mai arzikin man fetur da kuma samun goyon bayan wasu mayaƙan SPLM na Abdelaziz al-Hilu.














