Faransa tare da sama da abokan hulɗa 30 na kasa da kasa sun yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa fararen hula, asibitoci da ayyukan agaji a Sudan. Kasashen sun bayyana wadannan matakai a matsayin munanan take dokokin jin kai na kasa da kasa, tare da gargadin cewa wasu na iya zama laifukan yaki.
Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya sake jaddada bukatar tsagaita wuta nan take, kariyar fararen hula da kuma bai wa kungiyoyin agaji damar kai taimako ba tare da tangarda ba. Wannan matsaya na kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a ranar 18 ga Fabrairu 2026, wadda kasashe da dama na Turai da ma wasu na waje suka rattaba hannu a kai.
Sanarwar ta nuna damuwa kan tsanantar fada a yankunan Kordofan da Darfur, inda hare-haren sama da na jiragen marasa matuki suka shafi ‘yan gudun hijira, cibiyoyin lafiya da ayarin abinci. Haka kuma an ruwaito hare-hare kan motocin da rumbunan abinci na Hukumar Abinci ta Duniya (WFP), lamarin da ya jawo asarar rayuka da lalata muhimman kayayyakin more rayuwa.
Kasashen da suka sanya hannu sun bukaci dukkan bangarorin rikicin da su dakatar da fada, su kare fararen hula, musamman mata da yara, tare da amincewa da bincike mai zaman kansa kan take hakkin dan Adam. Sun kuma jaddada goyon bayansu ga kungiyoyin agaji da ke aiki a cikin mawuyacin hali.
Majiyar Labari: AA














