Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da tura sababbin jakadun Najeriya zuwa manyan ƙasashe uku na duniya – Amurka, Birtaniya da Faransa – a wani muhimmin mataki na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya ta ƙasar da ƙasashen waje.
A wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, an tabbatar da cewa Ambasada Ayodele Oke zai wakilci Najeriya a Faransa, yayin da Kanal Lateef Are zai zama Ambasada a Amurka. Haka kuma, Ambasada Aminu Dalhatu, tsohon jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu, an naɗa shi a matsayin Babban Kwamishinan Najeriya a Birtaniya.
Shugaba Tinubu ya umurci Ma’aikatar Harkokin Waje da ta sanar da gwamnatocin ƙasashen uku bisa ƙa’idar diflomasiyya, domin kammala dukkan matakan karɓar su a hukumance.
A ranar 18 ga Disamba, 2025, Majalisar Dattawa ta tabbatar da jakadu 64 da Shugaban Ƙasa ya naɗa, bayan duba rahoton Kwamitin Harkokin Waje. Tun da farko kuma, Tinubu ya tura jerin sunayen jakadu 65 zuwa Majalisa, waɗanda suka haɗa da na ma’aikata da kuma na siyasa.
Wannan sabon tura jakadu na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa martabar Najeriya a idon duniya da kuma bunƙasa hulɗar siyasa, kasuwanci da tsaro da manyan ƙasashe.














