Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cire sunayen wasu daga cikin wadanda ya yi wa afuwa a farkon watan nan.
Afuwar da Shugaban Kasar ya yi wa mutum 175 da kotuna suka yanke wa hukunci kan laifukan da suka aikata, ta jawo ce-ce-ku-ce sosai a fadin kasar.
Abin da ya fi daukar hankali a lokacin da aka sanar da afuwar shi ne ganin sunayen mutanen da suka aikata manyan laifuka, cikin wadanda aka yafewa, musamman manyan masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi, da masu kisan kai, da masu garkuwa da mutane, da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, da gaggan masu cin hanci da rashawa.
Sai dai sanarwar da Fadar Shugaban Kasar ta fitar a ranar Laraba ta ce bayan tuntuba da tattaunawa da Majalisar Magabata ta Kasa da jin ta ra’ayoyin mutane a kan lamarin, Shugaban Kasar ya ba da umarnin sake nazarin jerin sunayen mutanen da aka yi wa afuwar karkashin dokar da ta ba shi iko ta sashe na 175 (1) da (2) ta kundin tsarin mulkin 1999.
“An cire sunayen mutanen da aka yanke wa hukunci kan manyan laifuka kamar su satar mutane don kudin fansa da laifukan da suka shafi ta’ammali da miyagun kwayoyi da safarar mutane da zamba da mallakar makamai ko amfani da su ba bisa ka’ida ba, da sauran su, daga jerin,” in ji sanarwar.
Sauya hukunci
Fadar Shugaban Kasar ta kara da cewa wasu kuma da aka yi wa afuwa tun da farkon, an sauya hakan zuwa sassauta musu hukuncin daurin da aka yanke musu.
“Wannan matakin ya zama dole ne saboda tsanani da kuma tasirin tsaro na wasu laifukan, da kuma bukatar a kula da jin dadin wadanda aka zalunta da kuma al’umma baki daya, da kuma bukatar kara kwarin gwiwar hukumomin tsaro da kuma bin dukkan abin da ya zama wajibi kasar,” in ji sanarwar mai dauke da sa hannu Bayo Onanuga, mai bai wa Shugaban Kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru.
An yi la’akari da tsari na adalcin shari’a da ya shafi bangare uku, wato wanda ake tuhuma, da wanda abin ya shafa da kuma kasa da al’umma wajen sake nazarin afuwar.
Tuni an aika jerin sunayen waɗanda suka cancanci cin gajiyar afuwa zuwa ga Hukumar Gidajen Yari ta Nijeriya don aiwatarwa bisa ga takardun sakin da aka sanya wa hannu, kamar yadda Fadar Shugaban Nijeriyar ta bayyana.
Bugu da ƙari, Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin a gaggauta mayar da Sakatariyar Kwamitin Ba da Shawara kan Jinƙai daga Ma’aikatar Ayyuka ta Musamman ta Tarayya zuwa Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya.
Sanarwar ta ce ya yi hakan ne domin tabbatar da cewa ayyukan da za a yi nan gaba sun yi daidai da abin da mutane ke tsammata da kuma mafi kyawun ayyuka.
Kazalika, Shugaba Tinubu ya kuma umarci Atoni Janar na Kasa da ya fitar da matakan da suka dace don amfani da ikon nuna tausayi, wanda ya haɗa da yin shawarwari na tilas da hukumomin gabatar da ƙara da suka dace.
Wannan zai tabbatar da cewa mutanen da suka cika sharuɗɗan doka da ƙa’idoji ne kawai za su ci gajiyar fitar da takardun sakin. Shugaban ya yaba da ra’ayoyin masu ruwa da tsaki da kuma jama’a kan wannan batu.
Shugaba Tinubu ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta yin gyare-gyare ga fannin shari’a da inganta harkokin shari’a a Nijeriya.














