Davos, Switzerland – Ana sa ran Shugaban Amurka Donald Trump zai gana da manyan shugabannin kamfanoni na duniya (CEOs) a birnin Davos a ranar Laraba, yayin taron shekara-shekara na World Economic Forum (WEF), inda manufofinsa kan kasuwanci, tsaro da siyasa suka mamaye ajandar taron.
Rahoton Reuters ya ce an gayyaci shugabannin manyan kamfanoni daga bangarori kamar bankuna, harkar kudi na zamani (crypto) da shawarwari (consulting) zuwa wata liyafa ta musamman bayan jawabin Trump. Ana kuma sa ran shugabannin kasashe 64 da wakilai fiye da 3,000 daga kasashe sama da 130 za su halarci taron, yayin da batun Greenland da sabbin haraji na Amurka ke tayar da muhawara a tsakanin kasashen Turai.














