Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce Ankara za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa tare da shiga tsakani don warware rashin fahimta da ke tsakanin ɓangaren gabashi da kuma yammacin na Libya, yana mai bayyana kyakkyawan fata game da yarjejeniyoyi na sake haɗe ƙasar wuri guɗa.
“Za mu ci gaba da taka rawar da muke yi a nan da kuma matsayinmu na masu shiga tsakani,” kamar yadda Fidan ya shaida wa manema labarai a Benghazi bayan kammala taruka a Tripoli da Benghazi a yayin ziyararsa a Libya.
Fidan ya ce ya samu ƙwarin gwiwa bayan ganawarsa da shugabannin ɓangarorin biyu da ke rikicin siyasa a Libya, yana mai cewa za su bayar da goyon baya sosai wajen haɗa kan ƙasar.
Ya ƙara da cewa Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayanta ga tattaunawa da kuma haɗin gwiwa tsakanin yankunan yamma da gabashin Libya tare da yin aiki don ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a ƙasar.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Fidan ya yi cikakken bayani game da ziyararsa zuwa Libya, tare da gode wa hukumomin Libya saboda karamcinsu da kuma tarbar da suka yi masa.
Fidan ya ce ya halarci taruka masu “muhimmaci da amfani” a babban birnin Tripoli da kuma gabashin birnin Benghazi, yana mai bayyana ziyarar a matsayin wani ƙudurin Turkiyya na samar da “tsarin Libya Ɗaya,” wanda babu bambanci tsakanin yankin yamma da gabas da kuma kuɗancin ƙasar.
“Turkiyya ba ta bambanta zaman lafiya da kwanciyar hankalin Libya da nata,” in ji Fidan.
“Yana da matuƙar muhimmanci ‘yan’uwanmu maza da mata na Libya su gina makomarsu cikin ‘yanci da aminci da kuma wadata.
Dangane da hangen nesa da shugabanmu Recep Tayyip Erdogan ya gabatar, za mu ci gaba da ƙarfafa tattaunawa da haɗin gwiwa tsakanin yankunan yamma da gabashin Libya tare da bayar da gudunmawa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata na Libya,” in ji shi.
An tattauna batun haɗin gwiwa da tsarin siyasa
A yayin ziyarar tasa, Fidan ya gana da Firaministan Libya Abd al-Hamid Dbeibeh don tattauna dangantakar ƙasashen biyu da tsarin siyasa na Libya da ci gaban yankuna da kuma batutuwan tsaro, kamar yadda ya bayana.
Kazalika ya tattaunawa da Mohamed al-Menfi, shugaban Majalisar Shugabancin Libya da Mohamed al-Miftah Takala, shugaban Majalisar Kasa.
Fidan ya ce ya tattauna batun haɗin gwiwar ƙasashen biyu da kuma abubuwan da ke faruwa a halin yanzu tare da Ibrahim Dbeibeh, mai bai wa Firaministan Libya shawara kan harkokin tsaron ƙasa da mukaddashin ministan tsaro Abdulsalam Zubi da ministan harkokin cikin gida Emad al-Trabelsi da mukaddashin babban hafsan soja Salah al-Namroush da kuma shugaban hukumar leken asiri na soja Mahmoud Hamza.
A Benghazi, Fidan ya gana da Khalifa Haftar, kwamandan sojoji a gabashin Libya da mataimakinsa, Janar Saddam Haftar da Kakakin Majalisar Wakilai Aguila Saleh da kuma Belkacem Haftar, shugaban Asusun Ci Gaba da Sake Gina Kasa na Libya.
Tarurrukan sun mayar da hankali kan batun siyasa da tsaro a Libya da kuma damar da za a samu wajen inganta haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, in ji Fidan.
Ya jaddada cewa Turkiyya na daukar haɗin gwiwar ƙasashen biyu a fannin tsaro a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da za su iya bayar da gudummawa ga zaman lafiyar Libya da tsaron yankin.
A wani ɓangare na ziyarar tasa, Fidan ya kuma ziyarci rundunar sojojin Turkiyya da ke Tripoli.
















