Gwamnatin Uganda ta bayar da umarnin katse intanet a faɗin ƙasar kwana biyu gabanin zaɓen shugaban ƙasa, inda Shugaba Yoweri Museveni ke neman tsawaita mulkinsa zuwa kusan shekaru 40. Hukumar Sadarwa ta Uganda (UCC) ta ce matakin ya zama dole domin dakile yaɗuwar labaran ƙarya, zamba da tayar da tarzoma a lokacin zaɓe.
A wata wasiƙa da ta aika wa kamfanonin sadarwa, UCC ta bayyana cewa za a fara katsewar intanet da ƙarfe 6:00 na yamma agogon ƙasar, kuma za ta ci gaba har sai an sake bayar da umarnin dawo da sabis ɗin. Hukumar ta ƙara da cewa muhimman ayyukan gwamnati ba za su shiga cikin katsewar ba.
Duk da wannan, gwamnatin Uganda a baya ta musanta shirin rufe intanet, tana cewa jita-jitar hakan ƙarya ce da ake yaɗawa domin tayar da tsoro. Sai dai a zaɓen 2021 ma an katse intanet gaba ɗaya, a lokacin da aka zargi gwamnati da maguɗi da kuma danniya ga ‘yan adawa, musamman magoya bayan fitaccen mawaƙi kuma ɗan siyasa Bobi Wine.
Matakin da aka ɗauka a yanzu na sake tayar da damuwa game da ‘yancin faɗar albarkacin baki da gaskiyar tsarin dimokuraɗiyya a Uganda yayin da zaɓe ke gabatowa.














