Afirka

Interpol Ta Jagoranci Kama Mutum 651 a Ƙasashe 16 na Afirka Kan Damfarar Intanet

A wani samame na makonni takwas, jami’an tsaro sun rushe babbar hanyar damfarar intanet da ta kwashe fiye da dala miliyan 45 daga jama’a.

Newstimehub

Newstimehub

19 Feb, 2026

e59abb2b0e9641a54f9c1d33eed69c549be618f02f846ca50b37eeff06bceeb5

A cewar Interpol, an kama mutum 651 a kasashe 16 na Afirka, bayan wani aiki da ya dauki tsawon makonni takwas daga watan Disamba zuwa Janairu. An ce kungiyar ta damfari mutane da dama mafi yawansu a Afirka sama da dala miliyan 45 ta hanyoyin zuba jari na bogi, damfarar kudin waya da kuma manhajoji na karya.

Masu bincike sun kuma kwace na’urori 2,341 tare da rufe adireshin intanet da masu aikata laifukan ke amfani da su wajen gudanar da damfara.

Shugaban sashen yaki da laifukan yanar gizo na Interpol, Neal Jetton, ya ce kungiyoyin sun jawo babbar asara ga mutane da kasuwanci ta hanyar alkawuran karya. Ya kuma bukaci duk wanda aka yaudara da ya kai rahoto ga hukumomin tsaro.

Kasashen da suka shiga aikin sun hada da Angola, Benin, Kamaru, Chadi, Gabon, Gambiya, Ghana, Ivory Coast, Kenya, Namibia, Nijeriya, Rwanda, Senegal, Uganda, Zambia da Zimbabwe.

Majiyar Labari: TRT HAUSA