Wata mummunar zaftarewar ƙasa ta afku a ƙasar Indonesia bayan ruwan sama mai ƙarfi ya rika sauka ba kakkautawa, inda aka binne unguwanni gaba ɗaya a yankin West Bandung na tsibirin Java. Lamarin ya girgiza al’umma, yayin da hukumomi ke ci gaba da aikin ceto cikin mawuyacin hali.

Hukumar ceto ta ƙasa (BASARNAS) ta ce aƙalla mutane 8 sun mutu, yayin da sama da 82 ke ci gaba da ɓacewa a ƙarƙashin ƙasa da laka. Zaftarewar ta faru ne da sassafe, bayan ruwan sama mai ƙarfi ya daɗe yana sauka, wanda ya sa ƙasa ta yi laushi ta zame.
Shugaban karamar hukumar yankin ya ce sojoji, ’yan sanda da masu sa kai suna aiki tare don gano waɗanda suka makale, duk da cewa yanayin ƙasa mai laushi da haɗarin sake zamewa na ƙara wahalar aikin.
Masana muhalli sun danganta yawaitar irin waɗannan bala’o’i da raguwar dazuzzuka, inda aka ce sare itatuwa da ayyukan hakar ma’adanai sun raunana ƙasa, suna hana ta riƙe ruwa yadda ya kamata.














