Zanga-zangar da aka fara domin nuna damuwa kan tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki a Iran ta rikide zuwa tashin hankali, inda aƙalla mutane shida suka rasa rayukansu a arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro a wasu sassan yammacin ƙasar.
Zanga-zangar ta fara ne a ranar Lahadi a Tehran, bayan da ‘yan kasuwa suka shiga yajin aiki domin nuna adawa da hauhawar farashi da tsawaitar matsin tattalin arziki. Daga bisani, ta yaɗu zuwa wasu birane da dama, inda ɗalibai da wasu ƙungiyoyi suka shiga jerin masu zanga-zangar.
A ranar Alhamis, kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito mutuwar mutane biyu a garin Lordegan, a lardin Chaharmahal and Bakhtiari, da kuma mutane uku a Azna, a lardin Lorestan, sakamakon arangama da jami’an tsaro. Rahoton ya ce ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, tare da cafke wasu da hukumomi suka bayyana a matsayin jagororin masu tarzoma, yayin da aka lalata gine-gine da dama.
Gidan talabijin na gwamnati ya kuma tabbatar da mutuwar wani matashi ɗan shekara 21, mamba na ƙungiyar Basij, wanda aka kashe a rikici da ya faru da daddare a garin Kouhdasht. Mataimakin gwamnan lardin Lorestan, Said Pourali, ya ce jami’an tsaro 13, ciki har da ‘yan sanda da mambobin Basij, sun jikkata sakamakon jifa da duwatsu.
Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi yunƙurin kwantar da hankula ta hanyar amincewa da halaccin wasu daga cikin koke-koken masu zanga-zangar, yana mai kiran gwamnati da ta ɗauki matakan rage wahalhalun tattalin arziki. Sai dai hukumomi sun jaddada cewa za su dauki mataki mai tsauri kan duk wani tashin hankali ko lalata dukiyar jama’a.
A wani bangare, kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ce an kama mutane bakwai da ake zargi suna da alaƙa da ƙungiyoyin da gwamnati ke kira “maƙiyan Iran” a Amurka da Turai, bisa zargin ƙoƙarin karkatar da zanga-zangar zuwa tarzoma. Wannan na zuwa ne yayin da darajar kuɗin Iran ta faɗi da fiye da kashi ɗaya cikin uku a kan dalar Amurka a cikin shekara guda, lamarin da ya tsananta tsadar rayuwa.














