Ministan Tsaro mai jiran rantsuwa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa da zarar ya hau kujerar ministan tsaro, wajibi ne a dakatar da tattaunawa da kuma biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga a Najeriya. A jiya yayin tantancewarsa a Majalisar Dattawa, Janar Musa ya ce ba za a samu cikakken ci gaba wajen yaki da rashin tsaro ba sai an kafa ingantaccen rumbun bayanan ’yan kasa wanda zai haɗa bayanai da tsaro, banki, da tsarin tantance mutum.
Tantancewar tasa ta zo ne a daidai lokacin da Majalisar Wakilai ta bukaci a riƙa gudanar da shari’o’in ta’addanci a bainar jama’a domin rage karuwar laifukan ta’addanci da tashin hankali. A jawabinsa, Janar Musa ya jaddada cewa gwamnati dole ta nisanci duk wata tattaunawa da masu ta’addanci domin hakan na ƙara musu ƙarfin gwiwa ne kawai.





