Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na haɗin gwiwa da ke aikin tabbatar da zaman lafiya sun kai samame a kan wani da ake zargin yana safarar makamai a jihar Plateau. Samamen ya gudana ne a Gashish ranar 3 ga Disamba, 2025, bayan samun ingantattun bayanai game da ayyukan wanda ake nema a kauyen Ranbiri na ƙaramar hukumar Barkin Ladi.
Ko da yake mutumin ya gudu kafin isowar sojojin, binciken da aka gudanar a gidansa ya taimaka wajen gano muhimman abubuwa, ciki har da bindigogi irin su AK-47. Rundunar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da bin diddigin wanda ya tsere domin cafke shi, tare da tsaurara matakan tsaro don hana aikata laifuka da safarar makamai a yankin.














