Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Nijeriya, NAFDAC, ta fitar da gargaɗin jama’a kan janye Indomie Vegetable Flavour noodles, biyo bayan gano sinadarai masu haddasa rashin lafiyan jiki da ba a bayyana ba, waɗanda ka iya jefa masu amfani cikin barazana. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, Darakta-Janar ta NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta bayyana cewa samfurin da abin ya shafa ba ya kasuwa a halin yanzu a Nijeriya, amma duk da haka hukumar ta ƙara tsaurara sa ido domin hana shigowarsa ƙasar ko yaduwa a kasuwanni.
Ta ce NAFDAC ta umarci daraktoci na shiyyoyi da jami’an jihohi da su ƙara bincike a duk faɗin ƙasar tare da kwashe samfurin idan aka gano shi, yayin da sashen binciken tashoshin shigo da kaya (Ports Inspection Directorate) ke cikin shirin ko-ta-kwana domin hana shigo da duk wani nau’in noodles da aka janye ko wanda ba a amince da shi ba. Sanarwar ta jaddada cewa noodles na cikin jerin kayayyakin da gwamnatin tarayya ta haramta shigo da su ƙasar, lamarin da ke rage yiwuwar samfurin shiga kasuwar Nijeriya, duk da cewa NAFDAC ta ci gaba da tsaurara matakan sa ido a matsayin kariya.
Adeyeye ta yi kira ga masu amfani da su yi taka-tsantsan, su zubar da samfurin nan take idan suka gan shi, tare da kai rahoton duk wata sayarwa ko rarrabawa ga ofishin NAFDAC mafi kusa ko ta layin kyauta 0800-162-3322, sannan su kai rahoton duk wata illa da ta taso ta shafukan E-reporting na hukumar.














