Siyasa Duniya

Cambodia da Thailand sun shiga tattaunawar sasanta rikicin iyaka

Cambodia da Thailand sun fara tattaunawa ta kwanaki huɗu domin sasanta rikicin iyaka da ya sake ɓarkewa a farkon watan Disamba.

Newstimehub

Newstimehub

24 Dec, 2025

download 6 e1766607839373

A wani mataki na rage zafin rikicin da ya sake ɓarkewa, ƙasashen Cambodia da Thailand sun soma tattaunawa ta tsawon kwanaki huɗu, da fatan samar da mafita ga takaddamar iyaka da ke barazana ga zaman lafiya a tsakaninsu.

Tattaunawar na gudana ne a lardin Chanthaburi na Thailand, duk da cewa Cambodia ta nemi a gudanar da zaman a wani wuri na tsaka-tsaki.

Rikicin ya sake ɓarkewa ne a ranar 7 ga watan Disamba, bayan rushewar wata yarjejeniya da ministan harkokin wajen Thailand ya ce an yi gaggawar cimmawa karkashin shirin Amurka.

Ko da yake ɓangarorin biyu sun ruwaito kai wa juna hari a ranar Laraba, jami’ai daga kasashen sun bayyana kwarin gwiwa cewa tattaunawar, wadda za a kammala ranar Asabar, za ta haifar da daidaito.

Majiyar Labari: BBC Hausa