Hatsarin motar Anthony Joshua ya sake ɗaukar sabon salo, domin rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta tabbatar da cewa ta tsare direban motar da ya tuka lokacin da aka yi haɗarin da ya yi sanadin mutuwar abokansa biyu. Direban, wanda shima ya ji rauni a hatsarin, an kama shi ne bayan an sallame shi daga asibiti, kamar yadda ’yan sanda suka tabbatar.
Hatsarin ya faru ne a kan hanyar Lagos–Ibadan lokacin da motar Lexus SUV da ke ɗauke da Anthony Joshua da abokansa Latif Ayodele da Sina Ghami ta yi karo da wata babbar mota da ke tsaye a gefen hanya. Daga cikin fasinjojin, Ayodele da Ghami sun mutu nan take, yayin da Joshua da direban suka tsira da raunuka kaɗan.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Ogun, Oluseyi Babaseyi, ya ce direban yana hannunsu yanzu kuma ana gudanar da bincike. Hukumar kula da zirga-zirga ta jihar ta ce binciken farko ya nuna cewa motar na tafe da gudu sosai kuma tayarta ta fashe kafin haɗarin ya faru.
Bayan an sallame shi daga asibiti, Joshua tare da mahaifiyarsa sun ziyarci dakin ajiye gawa domin yin bankwana da abokansa kafin a yi shirin kai gawawwakin ƙasar Birtaniya. Har yanzu ba a tabbatar da ainihin inda Joshua yake yanzu ba.














