Sabon matakin diflomasiyya ya sake tayar da kura a Yammacin Afirka bayan Benin da Nijar suka kori jami’an jakadun juna a matsayin ramuwar gayya, lamarin da ke nuni da ci gaba da dagulewar dangantaka tun bayan juyin mulkin soji da ya kifar da Mohamed Bazoum a 2023.
Nijar ta zargi Benin da kokarin dagula lamura a kasarta, zargi da Cotonou ta musanta, yayin da Benin ta kori jami’an diflomasiyya biyu na Nijar ba tare da bayyana dalili ba. A martani, Nijar ta ayyana wani babban jami’in diflomasiyyar Benin a Niamey a matsayin wanda ba a bukatarsa tare da ba shi awanni 48 ya bar kasar.
Dangantakar bangarorin ta kara sarkakiya ganin cewa Nijar na cikin kawancen AES tare da Mali da Burkina Faso, yayin da Benin ke nan cikin ECOWAS.














