Biyo bayan harin da ya girgiza al’ummar Kasuwan Daji a Jihar Niger, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki matakin gaggawa ta hanyar ba jami’an tsaro umarnin kamo dukkan masu hannu a kisan da sace-sacen da suka faru.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ministan Tsaro, Babban Hafsan Tsaro, hafsoshin rundunonin soji, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, da Darakta Janar na Hukumar DSS da su gano tare da cafke ’yan ta’addan da ake zargi da kai harin Kasuwan Daji a Jihar Niger.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi, Tinubu ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun ƙalubalanci juriyar Najeriya, tare da jaddada cewa dole ne su fuskanci hukunci mai tsanani bisa laifukan da suka aikata. Ya ce babu wanda zai tsira, ciki har da duk masu taimaka musu ta kowace hanya.
Shugaban Ƙasar ya kuma umarci hukumomin tsaro da su yi gaggawar ceto dukkan mutanen da aka sace, musamman mata da yara, a yayin harin. Umarnin ya biyo bayan rahotannin kisan manoma da fararen hula da wasu ’yan ta’adda da ake zargin sun tsere daga jihohin Sokoto da Zamfara bayan harin jiragen saman Amurka a daren Kirsimeti.
Tinubu ya yi Allah-wadai da harin, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, da kuma gwamnatin da al’ummar Jihar Niger. Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa an umarci jami’an tsaro da su ƙara kaimi wajen tsare al’ummomi masu rauni, musamman yankunan da ke kusa da dazuzzuka da ke zama mafakar ’yan bindiga.
Har ila yau, Shugaban Ƙasar ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu haɗin kai da jajircewa, yana gargadin cewa kalaman rarrabuwar kai na iya raunana tsaron ƙasa a wannan lokaci mai wahala. Ya ce haɗin kai ne kaɗai zai ba da damar dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da abin ya shafa.














