Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta bayyana cewa ta bankaɗo wasu kadarori har guda 41, masu darajar kusan Naira biliyan 212, waɗanda ake zargin suna da alaƙa da tsohon Ministan Shari’ar Najeriya, Abubakar Malami.
Rahoton jaridar TheCable ya ce kadarorin sun haɗa da otel-otel, gidajen zama, fulotai da makarantu, kuma an gano su ne a Abuja, Kano da kuma jihar Kebbi.
A cewar rahoton, an ƙiyasta kadarorin da ke Kebbi sun kai Naira biliyan 162.1, sai na Kano Naira biliyan 16, yayin da na Abuja suka kai Naira biliyan 34.6.
Tun da fari, gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara kan Malami da ɗansa Abdulaziz Malami, inda take tuhumarsu da laifuka 16 da suka shafi zamba da almundahanar kuɗi.














