Afcon 2025 Nijeriya Wasanni

Gaggawa: Super Eagles Sun Doke Algeria, Sun Kai Wasan Dab da Na Ƙarshe na AFCON 2025

Super Eagles sun doke Algeria da ci 2–0 a kwata fainal, inda suka kai wasan dab da na ƙarshe na AFCON 2025.

Newstimehub

Newstimehub

11 Jan, 2026

SuperEagles vs tunisia

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta samu nasarar tsallakawa zuwa wasan dab da na ƙarshe na Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2025, bayan doke Algeria da ci 2–0 a wasan kwata fainal da aka buga a birnin Marrakech na ƙasar Morocco.

’Yan wasan da koci Eric Chelle ke jagoranta sun nuna bajinta, inda Victor Osimhen ya fara zura ƙwallo a ragar Desert Foxes da bugun kai bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, kafin Samuel Akor Adams ya ƙara ta biyu a minti na 57 da bugun ƙwallo mai kyau.

Tun kafin wasan, Super Eagles na cikin kyakkyawan yanayi bayan sun murƙushe Mozambique da ci 4–0 a zagayen ‘yan 16, lamarin da ya kai adadin ƙwallayensu 12 cikin wasanni huɗu — mafi yawa a gasar zuwa yanzu.

Da wannan nasara, Nijeriya za ta fafata da mai masaukin baki, Morocco, a wasan dab da na ƙarshe, yayin da burin ɗaga kofin ke ƙara bayyana ga Super Eagles.

Majiyar Labari: TVC NEWS