Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya, FCTA, ta sanar da cewa ta kwato mabarata da masu fama da larurar tabin hankali guda 607 daga titunan Abuja tsakanin watan Yuli 2025 zuwa Janairu 2026, a wani yunƙuri na tsaftace birnin da kuma kare lafiyar jama’a.
Shugabar sashen tilasta doka na Ma’aikatar Ci gaban Jama’a ta FCT, Malama Ukachi Adebayo, ta bayyana cewa aikin ya gudana ne ta hannun rundunar “Operation Sweep Abuja Clean”, inda aka yi wa mutanen nasiha, aka tattara bayanansu, sannan aka mika su zuwa ofisoshin jihohinsu domin a mayar da su gida don shirin gyara da kula da su. Ta kuma bayyana cewa duk da ana kwashe su, da yawa kan dawo tituna saboda matsalolin tsaro da talauci a jihohinsu.
FCTA ta cire mabarata 583 da masu larurar hankali 23 daga Abuja, ta yi musu nasiha, ta tattara bayanansu, sannan ta mayar da su jihohinsu don gyara. Hukumomin sun kuma bayyana cewa ana amfani da wasu yara wajen bara ta hanyar kasuwanci, inda ake kawo su daga wasu jihohi ba tare da sanin iyayensu ba.














