Seoul – Wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke wa tsohon Firayim Minista Han Duck-soo hukuncin daurin shekaru 23 a gidan yari saboda rawar da ya taka a yunkurin kafa dokar ta-baci a zamanin tsohon shugaban ƙasa Yoon Suk Yeol, wanda aka tsige daga mulki.
Kotun gundumar tsakiyar Seoul ta bayyana cewa ayyana dokar ta-baci a ranar 3 ga Disamba 2024 ya kai matsayin “tawayen gwamnati”, kuma wannan ne karo na farko da wani jigo a gwamnatin Yoon ya samu hukunci a wannan shari’a. Yoon kansa kuwa ya riga ya samu hukuncin shekaru biyar, yayin da ake sa ran kotu za ta yanke hukunci kan bukatar yanke masa hukuncin kisa a ranar 19 ga Fabrairu.














