Amurka ta kammala ficewarta daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a hukumance, matakin da ya kawo ƙarshen kusan shekaru 78 na kasancewarta mamba a babbar hukumar lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Wannan ficewa ya fara aiki ne daga ranar 22 ga Janairu, 2026, bayan cika wa’adin sanarwar shekara guda da dokokin kasa da kasa suka tanada.
Sakataren Harkokin Waje, Marco Rubio, tare da Sakataren Lafiya, Robert F. Kennedy Jr., sun bayyana cewa Amurka ta yanke shawarar barin WHO saboda abin da suka kira gazawar hukumar wajen tafiyar da annobar COVID-19, da kuma zargin nuna fifiko na siyasa, jinkirin musayar bayanai, da karkata ga muradun wasu ƙasashe.
A sakamakon haka, an dakatar da dukkan tallafin kuɗi da na ma’aikata daga Amurka ga WHO, tare da mayar da ma’aikatan ƙasar gida. Amurka ta ce yanzu za ta mayar da hankali ne kan haɗin gwiwa kai-tsaye da ƙasashen abokan hulɗarta a harkokin kiwon lafiya.
Daraktan Janar na WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana baƙin cikinsa kan wannan mataki, yana cewa ficewar Amurka ba ta amfani kowa ba, kuma zai iya shafar yaƙi da manyan cututtuka a duniya.














