Ofishin jakadancin United States a Abuja ya soke dukkan alƙawuran neman biza na ranar 4 ga Maris 2026, saboda yiwuwar zanga-zanga a babban birnin Nigeria. Ofishin ya gargadi ‘yan Amurka da ke Abuja su kasance a gidajensu saboda barazanar tarzoma sakamakon rikicin da ke gudana tsakanin Amurka da Iran.
Matakin ya biyo bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, wanda ya yi sanadin mutuwar jagoran addinin kasar Ali Khamenei da wasu manyan jami’an Iran. Iran ta mayar da martani da harba makamai masu linzami kan sansanonin Amurka a kasashen Gulf, tare da bayyana cewa za ta dauki fansa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi wuri ga Iran ta nemi tattaunawa, yana mai cewa hare-haren sun yi mummunar illa ga karfin sojin Iran. Sai dai Tehran ta ce ba ta da wani dalili na yin wata tattaunawa da Amurka, tana mai jaddada cewa rikicin na iya ci gaba muddin bukata ta taso.














