Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Nijeriya ta karɓi ‘yan ƙasar 708 da suka maƙale a Jamhuriyar Nijar, waɗanda aka kwaso daga birnin Niamey.
Mutanen sun iso ne filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda jami’an gwamnati suka tarbe su, suka yi rajista tare da tantance su.
Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban Ayyuka na NEMA a Kano, Dakta Nura Abdullahi ya ce waɗanda aka dawo da su sun haɗa da maza da yara 292 da mata da yara 416 daga jihohi daban-daban na ƙasar.
“Ma’aikatar Harkokin Waje ta Tarayya ce ta jagoranci wannan shiri na kwaso mutanen,” in ji Abdullahi. “An tanadar musu da abinci, matsuguni na wucin-gadi, da sauran kayan agaji na gaggawa.”
Ya ƙara da cewa an ba su barguna, gidajen sauro, da kuma kayan kula da kai da suka haɗa da kayan tsafta, zannuwa, audugar mata, da sauran muhimman kayayyaki.
Ƙungiyar Agaji ta Nigerian Red Cross Society ta kula da marasa lafiya daga cikin waɗanda aka dawo da su, yayin da aka tura masu buƙatar kulawa ta musamman zuwa asibitoci.
Abdullahi ya shawarci matasa da su guji yin hijira mai haɗari. Ya ce, “Ya kamata matasan Nijeriya su daina saka rayuwarsu cikin haɗari wajen neman dama a ƙasashen waje ba tare da tsari mai kyau ba.”
A nata bangaren, jami’ar kula da ofishin Kano na hukumar kula da ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani ta ƙasa, Hajiya Luba Liman ta bayyana aikin a matsayin haɗin gwiwar dukkan ɓangarorin gwamnati.
“Wannan dawowa ne bisa son ransu. Da dama ba su da kuɗin dawowa gida, shi ya sa gwamnati ta shirya kwaso su,” in ji ta, tana mai nuni da haɗin gwiwa da ofishin jakadancin Nijeriya da ke Niamey.
Jami’ai daga NCFRMI, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, da kuma Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya sun halarci wajen tarbar waɗanda aka dawo da su.














