A birnin Niamey, dalibai da matasa sun hallara a wani taron tattaunawa domin duba rawar da za su taka wajen kare yankin Sahel. Taron, wanda ƙungiyar daliban jami’ar Université Abdou Moumouni de Niamey ta shirya, ya mayar da hankali kan muhimmancin hadin kan matasa wajen tabbatar da tsaro a yankin Alliance des Etats du Sahel (AES).
A wajen taron, shugabannin dalibai sun jaddada cewa matasa na da rawar gani wajen kare ƙasa, ba wai kawai ta fuskar shiga aikin tsaro ba, har ma wajen bayar da bayanan sirri da kuma kasancewa masu lura da abubuwan da ke faruwa a al’umma. Sakataren ƙungiyar, Issoufou Garba Idrissa, ya bukaci matasa su kasance cikin shiri domin amsa kiran ƙasa idan bukatar hakan ta taso, yana mai cewa dole ne a yi hakan cikin tsari da bin umarnin hukumomi.
Ya kuma bayyana cewa duk da akwai rundunar sojoji da ke aiki, tana fuskantar ƙalubale, don haka idan an buƙaci ƙarin taimako daga matasa, ya kamata su kasance a shirye. Bugu da ƙari, ya jaddada muhimmancin kula da bayanai da kuma rawar da matasa za su taka wajen inganta tsaro ta hanyar sadarwa da wayar da kai.
Taron ya haɗa dalibai, matasa da kuma ’yan jarida, inda aka yi muhawara da musayar ra’ayoyi kan yadda za a ƙarfafa tsaro da haɗin kai a yankin Sahel.
MAJIYAR LABARI: AGENCE NIGERIENNE DE PRESSE















