Nijeriya

Jam’iyyar adawa ta NDC a Nijeriya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu game da rijistarta

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan wata babbar kotun tarayya a birnin Lokoja ta jihar Kogi, ta jingine hukuncin da ta yanke daga farko da ya bai wa hukumar zaɓe (INEC) umarnin yi wa NDC rijista a matsayin jam’iyyar siyasa.

Newstimehub

Newstimehub

30 Jun, 2026

4a6131ff6811754058898357b87befc9457098bf3584f19cb9980be0589e716c

Jam’iyyar hamayya ta NDC a Nijeriya, ta ɗaukaka ƙara bisa hukuncin da wata kotu ta yanke wanda ta soke umarnin da ta bai wa hukumar zaɓen ƙasar, INEC, na yi wa NDC rijista a matsayin jam’iyyar siyasa a baya.

Wannan na zuwa ne kwanani bayan wata babbar kotun tarayyar Nijeriya da ke zama a birnin Lokoja na jihar Kogi ta jingine hukuncin janye umarnin yi wa NDC rijista.

Hukuncin ya biyo bayan wata ƙarar da jam’iyar PMP ta shigar, inda ta nemi a jingine hukuncin na watan Disambar shekarar 2025 saboda ba a saka ta cikin batun ƙarar ba.

Alƙalin kotun, Isah Dashen, ya amince da ƙarar PMP kuma ya yanke hukuncin cewa dole a ji ta bakin dukkan masu ruwa-da-tsaki kan lamarin kafin a iya yanke hukunci a kansa.

Alƙalin ya ayyana cewa irin wannan mantuwa ta sa lamarin gabaɗaya ya saɓa wa doka, kuma ya yanke hukuncin cewa dole lamura su koma yadda suke a da, kafin watan Disambar shekarar 2025, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci game da lamarin.

Ɗaukaka ƙara

A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin da dare, shugaban jam’iyyar NDC na ƙasa, Seriake Dickson, ya ce jam’iyyar tana kuma neman a dakatar da aiwatar da hukuncin kotun.

Dickson, wanda shi ne ɗantakarar jam’iyyar NDC a zaɓen sanata na mazaɓar Bayelsa ta Yamma a majalisar dattawan Nijeriya, ya bayyana cewa an bai wa shugaban hukumar INEC da jami’ansa kwafi na ɗaukaka ƙarar “domin su yi abin da ya dace bisa doka da kuma abin da ya dace a hankali a bisa doka.”

“Bayan mun shigar da ƙara kuma mun miƙa ɗaukaka ƙararmu da sauran takardun, yanzu kallo zai koma ɓangaren shari’a ne, kuma muna tsammanin ɓangaren shari’a zai yi abin da ya dace a ƙarƙshin doka,” in ji shi.

Jagoran jam’iyar na ƙasa ya kuma tabbatar da cewa , bayan ɗaukaka ƙarar, INEC ta bai wa jam’iyyar NDC damar saka ‘yantakararta a shafin INEC na intanet.

“An ba mu damar shiga shafin (na INEC) domin saka ‘yantakararmu da suka cancanta.

“An saka sunana da na ɗantakarar shugabanƙasa (Peter Obi) a shafin na INEC, yayin da za a saka na ɗantakarar mataimakin shugaban ƙasa gobe (Talata),” in ji shi.

Bayanan cikin ɗaukaka ƙarar

Seriake Dickson dai bai ba da bayanan cikin ɗaukaka ƙarar ba, ciki har da kotun da aka shigar da ɗaukaka ƙarar.

Sai dai jaridar Premium Times ta ruwaito cewa NDC ta shigar da ƙarar ne a kotun ɗaukaka ƙara da ke Lokoja, a jihar Kogi.

Kawo yanzu, babu tabbacin ko kotun ɗaukaka ƙarar ta tsayar da ranar fara sauraron ƙarar.