Aƙalla mutane 14 ne suka mutu a wani hari da aka kai a jihar Benue ta Nijeriya a ranar Talata, yayin da wasu da dama suka jikkata, a cewar wani jami’in yankin.
Jihar Benue ta ta jima tana fuskantar rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, inda ɗaruruwan mutane suka mutu a shekarun baya bayan nan, kuma rahotanni sun nuna cewa manoma na kai hari kan shanun da ke lalata amfanin gona kana su kuma makiyaya ke kai hari kan ƙauyukan.
Harin na baya bayan nan ya faru ne a ƙauyen Efeyi da ke yankin Otukpo na jihar da sanyin safiyar ranar Talata, inda ‘yanbindiga suka kashe mutane 14 tare da jikkata mutane da dama, kamar yadda shugaban Ƙaramar Hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Ogiri ya ɗora alhakin harin kan makiyaya, sai dai ƙungiyoyin Fulani sun sha yin watsi da irin wannan zargi na kai hare-hare a baya.
Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.
Mai magana da yawun ‘yansandan jihar Benue, Udeme Edet, ya ce an tura jami’ai zuwa yankin da abin ya shafa kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

















