Gwamnan Babban Bankin Ghana (BoG), Dr Johnson Pandit Asiama ya tabbatar wa ‘yan kasar, musamman al’ummar Kirista, cewa tsarin banki da ba ya karɓar ruwa da Ghana ke shirin aiwatarwa ba wata hanya ba ce ta inganta ko yada wani addini a kasar ba.
Dr Asiama ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin wata ganawa da shugabannin addinai a Accra, inda ya yi ƙarin bayani kan tsarin dokoki da ka’idojin da za su jagoranci gudanar da bankin da ba ya karɓar ruwa.
Kazalika ya ce tsarin wani nau’in harkar kuɗi ne na kasuwanci wanda kowa zai iya amfana da shi ba tare da la’akari da addininsa ba.
“Babu wani addini da aka dora wa alhakin kula da ayyukan bankin, kuma babu wani sabon mataki daga wani addini da aka shigar a tsarin gudanarwar bankin,’’ in ji Asiama, yana mai kari da cewa bankin zai inganta tsarin hada-hadar kuɗi bisa ka’idojin ɗoka ta shekarar 2016 wato ‘‘Banks and Specialised Deposit Taking Institutions Act.’’
“Aikinmu kawai shi ne samar da tsarin dokoki da kulawa da cibiyoyin da ke da lasisi za su iya gudanar da wannan tsarin banki na kasuwanci wanda ya bai wa kowa da kowa dama ba tare da nuna bambanci ba.’’
















