Najeriya

EFCC ta bayana dalilen da ya sa manyan shari’o’in cin hanci ke ɗaukar lokaci kafin su kai kotu

Hukumar EFCC ta ce jinkirin kai manyan shari’o’in cin hanci kotu na faruwa ne saboda tsananin bincike da tattara hujjoji, ba wai sakaci ba.

Newstimehub

Newstimehub

12 Jan, 2026

EFCC HQ

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (EFCC) ta bayyana cewa jinkirin kai wasu manyan shari’o’in cin hanci kotu ba alamar rashin aiki ba ne, illa dai yana da alaƙa da wahalar bincike da tattara sahihan hujjoji, musamman idan lamarin ya shafi manyan jami’an gwamnati.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels Television a shirin Sunday Politics. Ya ce binciken laifukan da suka shafi manyan mutane masu riƙe da muƙamai ko cin hanci a fannin gwamnati na ɗaukar lokaci sosai kafin a kai ga gurfanar da su.

A cewarsa, “A cikin awanni 48 zan iya bincike tare da gurfanar da mai aikata laifin yanar gizo, amma idan maganar manyan mutane ce ko cin hanci a gwamnati, dole sai an yi cikakken shiri kafin a kai ƙara kotu.”

Olukoyede ya ƙara da cewa akwai ƙalubalen doka da na ƙasashen waje, musamman idan kadarori ko kuɗaɗe suna waje, lamarin da ke ƙara tsawaita bincike.

Ya musanta zargin da wasu ke yi cewa EFCC na nuna bambanci ko tana kai hari ga ’yan adawa kawai, yana mai cewa irin waɗannan zarge-zargen ba su dace da manufofin hukumar ba.

Ya ambaci batun tsohon Ministan Shari’a kuma Tsohon Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, inda ya ce binciken da ake yi ba shi da alaƙa da siyasa ko ƙiyayya ta kashin kai.

“Idan Nijeriya za ta ci gaba, dole mu yarda cewa yaƙin da ake yi da cin hanci dole ne ya kasance ba tare da son zuciya ko bangaranci ba,” in ji Olukoyede.

Majiyar Labari: Channels News