Kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC) ya fitar da gargaɗi ga jama’a kan sakonnin yaudara da ake turawa ta waya da ke cewa ana mayar da kuɗin bill ɗin wuta. IBEDC ta ce waɗannan sakonni ba daga gare ta suke fitowa ba, kuma ana amfani da sunan kamfanin ne kawai don yaudarar mutane su danna hanyoyin haɗi (links) na zamba.
Kamfanin ya bayyana cewa yawancin sakonnin suna zuwa ne da sunan mai aikowa “FROM: IBEDC”, suna cewa an sake lissafa kuɗin wuta kuma ana mayar da kuɗi ta wata shafin yanar gizo kamar www.infodhe.online, wanda IBEDC ta bayyana a hukumance a matsayin shafin yaudara. Kamfanin ya nanata cewa baya gudanar da wani shirin mayar da kuɗi ta irin wannan hanya, kuma babu alaƙa tsakaninsa da irin waɗannan hanyoyi.
IBEDC ta shawarci jama’a su yi hattara, kada su ba da bayanan banki, BVN, OTP, katin ATM ko kowace irin bayanan sirri ga irin waɗannan shafuka ko mutanen da ke kiran kansu jami’an kamfanin. Ta kuma jaddada cewa duk ma’amaloli na gaskiya kamar sayen wuta, bayanan asusu ko ainihin mayar da kuɗi su kasance ne kawai ta hanyoyin IBEDC na hukuma, irin su iRecharge, wakilai da aka amince da su, ko ofisoshin kamfanin.
IBEDC ta kuma bukaci jama’a su rika kai rahoton duk wani sako ko kiran da ake zargin zamba kai tsaye ga tashoshin kula da abokan cinikin kamfanin.














