Najeriya Tsaro

Janar Musa ya tabattar da a zamaninsa babu wanda zai ƙara biyan kuɗin fansa ko tattaunawa da ƴanbindiga

Janar Musa ya nuna cewa tsayin daka da ingantaccen tsarin bayanai ne ginshiƙin magance matsalar tsaro.

Newstimehub

Newstimehub

4 Dec, 2025

f4e8ac8f ce57 4bce a4cb d78ed9acd7e8.jpg e1764842333613

Ministan Tsaro mai jiran rantsuwa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa da zarar ya hau kujerar ministan tsaro, wajibi ne a dakatar da tattaunawa da kuma biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga a Najeriya. A jiya yayin tantancewarsa a Majalisar Dattawa, Janar Musa ya ce ba za a samu cikakken ci gaba wajen yaki da rashin tsaro ba sai an kafa ingantaccen rumbun bayanan ’yan kasa wanda zai haɗa bayanai da tsaro, banki, da tsarin tantance mutum.

Tantancewar tasa ta zo ne a daidai lokacin da Majalisar Wakilai ta bukaci a riƙa gudanar da shari’o’in ta’addanci a bainar jama’a domin rage karuwar laifukan ta’addanci da tashin hankali. A jawabinsa, Janar Musa ya jaddada cewa gwamnati dole ta nisanci duk wata tattaunawa da masu ta’addanci domin hakan na ƙara musu ƙarfin gwiwa ne kawai.