Najeriya ta bai wa Fernando Dias da Costa, ɗan takarar adawa a zaben Guinea-Bissau, mafaka a ofishin jakadancinta da ke Bissau, bayan rahotannin barazanar tsaro a kansa bayan juyin mulkin da sojoji suka yi. Wannan matakin ya fito ne daga wasiƙar Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, wacce ta nuna amincewar Shugaba Bola Tinubu wajen ba shi kariya. Najeriyar ta kuma nemi ECOWAS da ta tura tawagar ESSMGB domin tabbatar da tsaronsa a cikin harabar jakadancin.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin rawar da take takawa wajen kare zaman lafiya da dimokuraɗiyya a yankin. Wannan na zuwa ne bayan sojoji a Guinea-Bissau sun ayyana kifar da gwamnatin Umaro Sissoco Embalo tare da naɗa Janar Horta Inta-A a matsayin shugaban rikon ƙwarya na shekara ɗaya. A halin yanzu jam’iyoyin siyasa biyu – na Embalo da na Dias – suna ikirarin samun nasara yayin da ake jiran sakamakon zaɓen ranar 23 ga Nuwamba.
ECOWAS da Tarayyar Afirka sun dakatar da Guinea-Bissau saboda juyin mulkin, sannan suka tura tawagar sulhu domin tattaunawa da shugabannin sojin da ke mulki. Embalo kuma ya tsere zuwa Senegal kafin ya isa Jamhuriyar Congo, yayin da Najeriyar ke bayyana damuwa game da yiwuwar rikicewar ƙasar.






