Sabuwar matsala ta sake afkuwa a kan National Grid, lamarin da ya jefa sassa da dama na ƙasar cikin duhu. Kamfanonin rarraba wuta sun tabbatar da faruwar lamarin, suna cewa ana ci gaba da aiki don dawo da wutar lantarki a hankali.
Rahotanni sun nuna cewa wannan karin rugujewar grid ɗin na cikin jerin matsalolin da ake fama da su a shekarar 2025 duk da alkawuran gwamnatin tarayya. A halin da ake ciki, karamin kaso ne kawai na wuta ke isa ga masu amfani a sassa daban-daban na ƙasar.
Bayanan Rarraba Wuta – 29 ga Disamba, 2025 | 3:12 na Rana
Ibadan DisCo: 30MW
Abuja DisCo: 20MW
Sauran DisCos: 0MW
Abuja DisCo ta bayyana a shafinta na X cewa “wani tangarda ta faru a kan National Grid misalin 14:02pm, wanda ya janyo katsewar wuta a yankunan da muke kula da su. Muna aiki tare da hukumomin da abin ya shafa don maido da wuta cikin hanzari.”
Sai dai Eko DisCo ta ce an fara dawo da grid ɗin, kuma wuta tana komawa a hankali a wasu yankuna. Har yanzu Transmission Company of Nigeria (TCN) ba ta fitar da sanarwa ba.
Wannan na zuwa ne duk da kokarin gwamnatin tarayya da ta bayyana cewa tana kan tattaunawa kan rongi na dala miliyan $238 daga Japan (JICA) don inganta tsarin wutar lantarki, ciki har da:
ƙarin layukan 330kV da 132kV
sababbin manyan tashoshin wuta
inganta tsarin wutar kasa baki ɗaya
Masana na ganin wannan matsala tana sake bayyana irin kalubalen da tsarin wutar lantarki ke fuskanta a Najeriya duk da ƙoƙarin gwamnati.














