Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya tabbatar da kudirin rundunar na ƙara ƙarfafa tsaro a Jihar Neja ta hanyar tura ƙarin dakarun soja da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Soji, Kanal Appolonia Anele, ta fitar bayan ziyarar ban girma da Shugaban Sojin ya kai wa Etsu Nupe, Alhaji Dr. Yahaya Abubakar, a fadarsa da ke Bida.
Laftanar Janar Shaibu ya bayyana cewa ziyarar ta bai wa rundunar dama ta tantance halin da ayyukan tsaro ke ciki a jihar, gano gibin da ke akwai da kuma wuraren da ke bukatar ƙarin dakarun tsaro da tallafin ayyuka.
Ya jaddada muhimmancin bayanan leken asiri na cikin al’umma da na kai tsaye, yana mai bayyana sarakunan gargajiya a matsayin muhimman abokan hulɗa wajen samar da bayanan tsaro cikin lokaci. Rundunar ta kuma bayyana shirin amfani da sabbin fasahohin sa ido da ayyukan tsaro domin inganta dabaru da saurin martani.
A nasa martanin, Etsu Nupe ya tabbatar da goyon bayan sarakunan gargajiya ga rundunar soji, musamman a fannin samar da bayanan leken asiri da addu’o’i domin nasarar ayyukan tsaro. Rundunar Sojin Najeriya ta sake nanata jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin aiki kafada da kafada da gwamnatoci, sarakunan gargajiya da al’ummomi domin dawo da zaman lafiya.














