Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawa ta musamman da Shugaban Rwanda, Paul Kagame, a birnin Paris, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan halin da duniya ke ciki da hanyoyin da Afirka za ta ci gaba a sabon yanayin duniya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Shugaban Rwanda Paul Kagame sun haɗu domin cin abincin rana na sirri a ranar Lahadi a Paris, inda suka tattauna batutuwan duniya da dabarun bunƙasa Afirka a daidai lokacin da sauye-sauyen duniya ke ƙara ƙarfi.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a tsara makomar Afirka, duk da ƙalubalen da ke tattare da canje-canjen tattalin arziki da siyasa a duniya. Ya ce sun yi duba kan halin da ake ciki a duniya da kuma rawar da Afirka za ta taka a sabon tsarin duniya.
A cewar mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, Tinubu na ci gaba da hutun ƙarshen shekara a Turai, gabanin tafiyarsa ta hukuma zuwa birnin Abu Dhabi na Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
An bayyana cewa Shugaban Ƙasar UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya gayyaci Tinubu domin halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week 2026 (ADSW 2026), wanda za a gudanar a farkon watan Janairu. Taron na tsawon mako guda na haɗa shugabanni daga gwamnatoci, kasuwanci da al’umma domin tsara sabbin hanyoyin bunƙasa ci gaba mai ɗorewa.
Taron na bana zai gudana ne da taken “The Nexus of Next: All Systems Go”, inda za a tattauna yadda za a haɗa ƙirƙira, kuɗi da jama’a domin samar da makoma mai ɗorewa ga duniya.














