A wani sabon yunƙuri na diflomasiyya domin kawo ƙarshen rikicin Gaza, Shugaban Amurka Donald Trump ya miƙa tayin haɗin gwiwa ga Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, inda ya gayyace shi ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza, matakin da ke nuna rawar da Turkiyya ke takawa a kokarin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Amurka Donald Trump, a matsayinsa na shugaban da ya kafa “Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza”, ya aikawa Shugaban Turkiyya Erdogan wasiƙa yana gayyatarsa ya zama memba na farko a kwamitin. Hukumar ta samu goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya bayan amincewa da shirin kawo ƙarshen yaƙin Gaza da tsagaita wuta. An kuma kafa kwamitin zartarwa da manyan jami’ai daga Turkiyya, Masar, Qatar, Birtaniya, Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu ƙasashe domin taimakawa wajen tsaro, mulki da sake gina Gaza a karkashin gwamnatin Falasɗinu ta wucin gadi.














