Nijar Siyasa

Wanene Moussa Tchangari — ɗan gwagwarmayar da ake ta kira a sako shi a Jamhuriyar Nijar.

Moussa Tchangari, fitaccen ɗan gwagwarmayar haƙƙin ɗan adam a Nijar, ya shafe shekara guda a tsare bayan kamun da aka yi masa bisa sukar gwamnatin soja, lamarin da ya jawo ƙara yawaitar kira a saki shi.

Newstimehub

Newstimehub

4 Dec, 2025

49a089d0 d0f8 11f0 9fb5 5f3a3703a365.jpg e1764853901806

A ranar 3 ga Disamba 2025 ne gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta kama Moussa Tchangari, ɗan gwagwarmaya, ɗan jarida, kuma sakatare janar na ƙungiyar Alternative Espaces Citoyens.
Jami’an tsaro cikin fararen kaya ne suka shiga gidansa da ke Yamai suka yi awon gaba da shi. An kama shi ne shekara guda bayan juyin mulkin da shugaban soja Abdurrahmane Tchiani ya yi wa gwamnatin farar hula ta Mohamad Bazoum. Tchangari ya shiga jerin mutum fiye da 50 da aka tsare tun bayan juyin mulkin watan Yuli 2023.

Bayan kama shi, ya shafe kusan wata ɗaya a hannun jami’an yaki da ta’addanci kafin a tura shi gidan kaso na Filingue, mai tazarar kilomita 180 daga Yamai. An zarge shi da “haɗa kai da ‘yan ta’adda”, “cin amanar bayanan sirri na ƙasa”, da “ba wa abokan adawa bayanai masu muhimmanci”. Wadannan tuhumar sun taso ne daga sukar da yake yi wa gwamnati—musamman kan batun komawa turbar dimokraɗiyya, ci gaban ƙasa, da matsalar tsaro a yankin Sahel.

Tchangari ya shafe sama da shekaru 30 yana fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, yaki da cin hanci, da neman ingantaccen shugabanci. A 2015 ma, a zamanin Mohammadu Issoufou, an taɓa kamawa bisa sukar yadda gwamnati ke tafiyar da yaƙi da Boko Haram da illolin ta’addanci kan fararen hula. Har ila yau, yana koyar da nazarin haƙƙin ɗan adam a Kwalejin Horar da ‘Yan Sanda ta Niamey. Ya kuma shahara a fadin yankin Sahel wajen jawabai da taruka da suka shafi dimokraɗiyya da ‘yancin ɗanadam.

Ƙungiyoyi da dama, ciki har da Amnesty International da ƙungiyar sa ta Alternative, suna ci gaba da neman a sake shi, suna mai cewa tsare shi na tauye haƙƙin ɗan adam. Iyalansa, musamman ‘ya’yansa Falmata da Yakaka Mariama sun fito fili suna shiga gangamin neman ‘yancinsa.