Ranar Lahadi ta koma ranar baƙin ciki ga al’ummar Bekkersdal da ke kusa da Johannesburg, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari wani gidan sayar da barasa suka buɗe wuta ba tare da tsoro ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum tara nan take, kamar yadda ‘yansandan Afirka ta Kudu suka tabbatar.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne a wani gari da ake hakar zinari, mai nisan kilomita 40 kudu maso yammacin Johannesburg. Aƙalla mutane goma sun jikkata, wasu na cikin mawuyacin hali. Da fari ‘yansanda sun ce mutum goma ne suka mutu, amma daga baya suka gyara adadin zuwa tara.
A cewar rundunar ‘yansanda, maharan sun iso ne cikin motoci biyu, suka buɗe wuta kan mutanen da ke wurin, sannan suka ci gaba da harbe-harbe a cikin gidan barasar kafin su tsere. Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu har da wani direban motar haya, in ji Kwamishinan ‘yansanda, Manjo Janar Fred Kekana.
Harin ya kasance na biyu irinsa a ƙasar cikin wata guda, abin da ke ƙara nuna yadda matsalar tashin hankali da amfani da makamai ke ƙara ta’azzara. ‘Yansanda sun ce sun fara farautar maharan ruwa-a-jallo tare da ci gaba da bincike.














