Isra’ila ta sanar da amincewa da Jamhuriyar Somaliland a hukumance a matsayin ƙasa mai ‘yanci da cikakken iko, lamarin da ya sanya ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta ɗauki wannan mataki, abin da ke iya sauya yanayin siyasa a yankin Kahon Afirka.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa za ta fara haɗin gwiwa da Somaliland a fannoni kamar noma, lafiya, fasaha da tattalin arziki, yana mai bayyana matakin a matsayin wani ɓangare na ruhin yarjejeniyar Abraham Accords. Ya kuma taya Shugaban Somaliland, Abdirahman Mohamed Abdullahi, murna tare da gayyatarsa ziyartar Isra’ila.
Shugaban Somaliland ya ce ƙasarsa za ta shiga yarjejeniyar Abraham Accords, yana mai bayyana hakan a matsayin mataki zuwa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Sai dai Somalia tare da Masar, Turkiyya da Jibuti sun yi Allah-wadai da matakin, suna jaddada goyon bayansu ga haɗin kan Somalia da gargaɗin cewa amincewa da yankunan da suka balle na iya barazana ga tsaron duniya.
Somaliland dai na gudanar da mulkinta cikin kwanciyar hankali tun 1991, amma har yanzu ba ta samu amincewa daga wata ƙasa ba kafin wannan matakin na Isra’ila.














