Siyasar Kano ta dauki zafi sosai yanzu, domin rahotanni na nuna cewa kowane lokaci daga yanzu Gwamna Abba Kabir Yusuf na iya sauya sheka daga NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya. Wannan batu ya yi karfi ne bayan wasu kusoshin siyasa da makusantansa sun fito fili suna kira gare shi da uban gidansa Rabiu Musa Kwankwaso da su koma APC domin cigaban jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa manyan kusoshin gwamnati da dama sun riga sun nuna goyon bayan wannan tsari, ciki har da Director of Protocol na gwamna Abdullahi Ibrahim Rogo, mai magana da yawun gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa da shugaban majalisar dokokin jihar Kano Jibril Ismail Falgore. Sun gudanar da taron manema labarai inda suka matsa lamba kan Gwamna Abba da Kwankwaso su shiga APC, suna cewa hakan zai kawo zaman lafiya da ci-gaba ga Kano.
Har ila yau rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan majalisar jihar da na tarayya daga Kano na jiran gwamna ne domin su bi sahunsa zuwa APC. Amma wannan yuwuwar sauya sheka ta haifar da tambayoyi masu zafi: shin Kwankwaso ne ke shirin tura shi APC kafin ya bi shi daga baya? Ko kuwa Gwamna Abba ne ke son yin gaban kansa ba tare da sahalewar jagorinsa ba? Idan ma ya shiga APC kuma jam’iyyar ta ba shi takara, shin Kwankwaso zai tsaya masa ko kuwa zai tsayar da wani dan takara don kayar da shi?
Masana siyasa na ganin cewa shiga APC na iya kawo karshen rikicin masarautar Kano da kuma sassauta rikice-rikicen siyasar jihar, kasancewar Abba mutum ne mai sassaucin hali. Sai dai wasu na gargadin cewa rabuwar Abba da Kwankwaso na iya raunana shi siyasa, domin Kwankwaso ne ke kare martabarsa tun da dadewa. Haka kuma, wannan mataki zai girgiza jiga-jigan APC na Kano kamar Abdullahi Ganduje, Barau Jibrin, Nasiru Gawuna da Murtala Garo, musamman idan rahoton da ke cewa Garo zai iya zama mataimakin gwamna a 2027 ya tabbata.














