Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gargadi Gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara da ya bayyana yarjejeniyar da suka yi a gaban Shugaba Bola Ahmed Tinubu, in ba haka ba shi kansa zai sanar wa jama’ar jihar. Wike ya yi wannan furuci ne a taron masu ruwa da tsaki a Eleme, inda ya ce ba zai bari a ƙara rikitar da jama’ar Rivers ba.
Wike ya ce yarjejeniyar siyasar da ya yi a matakin ƙasa ta amfanar da Rivers, musamman ganin yadda aka ba shi mukamin Minista da kuma yadda aka saka mutanen jihar a muhimman mukaman tarayya. Ya kuma gargadi ’yan siyasa daga waje da su guji tsoma baki a siyasar Rivers, yana mai cewa sai wanda ya san tsarin siyasar jihar zai iya shiga cikinta.
A cewarsa, “Idan bai faɗa wa mutanen Rivers yarjejeniyar ba, ni zan faɗa musu.” Ya kara da cewa jama’ar Eleme su ci gaba da marawa shugabanninsu baya tare da goyon bayan Shugaba Tinubu. Manyan shugabannin yankin sun nuna goyon baya ga Wike, inda suka yaba masa bisa ayyukan raya kasa da ya yi a lokacin da yake gwamna, tare da tabbatar da biyayyarsu ga shawarar siyasa da zai bayar.
Taron ya haɗa manyan shugabanni daga PDP da APC, inda wasu tsoffin shugabanni suka dawo sahu. Hakanan an mika wa Wike kyauta a matsayin yabo kan gudummawar da ya bayar ga ci gaban yankin Eleme.














