Najeriya

JAMB Ta Fara Sayar da Fom ɗin UTME da Direct Entry na 2026

Hukumar JAMB ta sanar da fara sayar da fom ɗin UTME da Direct Entry na shekarar karatu ta 2026/2027 tare da shimfiɗa ƙa’idoji da ranakun jarrabawa.

Newstimehub

Newstimehub

14 Jan, 2026

IMG 3296

Hukumar Shigar da Dalibai Manyan Makarantu ta Nijeriya (JAMB) ta sanar da fara sayar da fom ɗin jarrabawar UTME da kuma shigar kai-tsaye (Direct Entry) domin shekarar karatu ta 2026/2027. Hukumar ta ce rajista za ta fara ne daga ranar 26 ga Janairu zuwa 28 ga Fabrairu 2026, yayin da jarrabawar UTME za ta gudana daga 16 zuwa 25 ga Afrilu 2026.

JAMB ta jaddada cewa dukkan masu neman rubuta jarrabawar dole ne su mallaki Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) kafin rajista. Ta kuma ce dole ne ɗalibi ya kai aƙalla shekaru 16 zuwa ranar 30 ga Satumba 2026, sai dai ‘yan ƙasa da wannan shekaru za su fuskanci tantancewa ta musamman idan sun samu maki sama da kashi 80 cikin 100 a dukkan jarabawar da suka rubuta.

Ga masu neman Direct Entry kuwa, sayar da fom ɗin zai fara daga 2 ga Maris zuwa 25 ga Afrilu 2026 a ofisoshin JAMB na jihohi da shiyyoyi. Haka kuma za a gudanar da Mock-UTME (jarrabawar gwaji) a ranar 28 ga Maris 2026 ga waɗanda suka zaɓa.

Majiyar Labari: Channels News