Ministan Albarkatun Man Nijar, Hamadou Tini, ya gabatar da tsarin inganta fannin mai a gaban mambobin Majalisar Ceto Ƙasa (CNSP) da masu ruwa da tsaki. Kamfanin dillancin labarai na ANP ya ruwaito cewa tsarin ya ƙunshi muhimman matakai da nufin ƙarfafa zuba jari da inganta tafiyar da harkokin mai.
Tsarin ya tanadi ɓangarori bakwai, ciki har da haɓaka ayyukan neman mai, ƙarfafa jagoranci da inganta samun kayayyaki da ayyuka a sashen. Haka kuma an tsara samar da wata hukuma mai zaman kanta da za ta kula da sa ido da tabbatar da bin doka a ɓangarorin ɗanyen mai da raba tacaccen mai.
Dabarun sun kuma haɗa da bunƙasa kamfanonin cikin gida, tattara ƙwarewar ‘yan ƙasa, da buɗe ƙofa ga ƙwarewar waje a hankali. An kuma jaddada muhimmancin kare muhalli, la’akari da tasirin zamantakewa da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Ministan ya bayyana cewa tsarin ya yi daidai da manufofin sake fasalin ƙasa, yana mai cewa manufar ita ce ƙara gudunmawar fannin mai ga tattalin arziki tare da inganta shugabanci na gari da dorewar ci gaba.
Majiyar: TRT HAUSA














