Kungiyar World Islamic League ta yi kakkausar suka kan harin da aka kai a Diori Hamani International Airport da ke babban birnin Niger a karshen watan Janairu. A wata sanarwa da ta wallafa, ta jaddada cikakken goyon bayanta ga Nijar tare da yin watsi da tashin hankali da ta’addanci a kowane irin salo.
Harin ya auku ne da daddare, inda ‘yan bindiga suka kai farmaki kan sansanin soji na Base 101, lamarin da ya haifar da musayar wuta mai karfi kafin jami’an tsaro su dakile harin.
Ma’aikatar Tsaron Nijar ta ce an kashe ‘yan ta’adda 20 tare da kama wasu 11, yayin da sojoji hudu suka jikkata kuma wasu jiragen farar hula da ma’ajiyar alburusai suka lalace.
Shugaban kasar Abdourahamane Tiani ya yaba wa jami’an tsaro da abokan hulda na Rasha, tare da zargin shugabannin Emmanuel Macron, Patrice Talon da Alassane Ouattarada hannu a harin—zarge-zargen da Benin da Côte d’Ivoire suka musanta. Daga baya, kungiyar ta’addanci Daesh ta dauki alhakin harin ba tare da bayar da karin bayani ba.
Majiyar Labari: AA














