Najeriya Siyasa

NNPP Ta Soke Dakatarwar Shugaban Jam’iyyar Kano, Ta Ce Ba Ta Da Inganci

Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na NNPP ya bayyana dakatarwar Shugaban jam’iyyar Kano, Hashimu Dungurawa, a matsayin haramtacciya, mara inganci kuma ba ta da wani tasiri a doka.

Newstimehub

Newstimehub

31 Dec, 2025

NNPP

A wani mataki da ya jawo hankalin ‘yan siyasa a Kano, jam’iyyar NNPP ta fito fili ta nesanta kanta daga matakin da aka ce an ɗauka na dakatar da shugaban ta na jihar, tana mai cewa ba ta san da shi ba kuma ba ta amince da shi ba.

Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya bayyana dakatarwar Shugaban jam’iyyar a Jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, a matsayin ba bisa ƙa’ida ba, mara inganci kuma babu wani tasiri a kanta. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya fitar.

A cewar jam’iyyar, wasu ‘yan kwamitin zartarwa na NNPP daga gundumar Gargari da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ne suka sanar da dakatar da Dungurawa, bisa zargin cewa yana haddasa rabuwar kai da rikici a cikin jam’iyyar. Sai dai NWC ta ce wannan mataki ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar kuma yana nuna rashin ladabi da tsattsauran ra’ayin adawa da jam’iyya.

Bayan sanar da dakatarwar, shugabannin NNPP na Kano sun bayyana Abdullahi Abiya a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar a jihar, matakin da NWC ta ce shima ba shi da tushe balle makama.

Sanarwar ta bayyana dakatarwar a matsayin “mara tushe, rashin dimokiraɗiyya, null and void, kuma ba ta da wani tasiri kwata-kwata,” tana mai cewa hakan babban laifi ne a dokokin jam’iyyar.

Jam’iyyar NNPP ta yabawa Hashimu Dungurawa, inda ta bayyana shi a matsayin shugaba mai kishin aiki, jajircewa da ɗaukar nauyi, tare da jaddada cewa jagorancinsa ya taimaka matuƙa wajen bunƙasar jam’iyyar a Jihar Kano.

NWC ta ƙara da cewa za ta ɗauki duk matakan da suka dace domin kare mutuncin jam’iyyar da tabbatar da bin doka da oda a dukkan matakan shugabanci.

Majiyar Labari: ChannelsTV