A cikin wani gagarumin samame da ya girgiza yankin tsakiyar Mali, rundunar sojin ƙasar ta kai wani mummunan harin sama a cikin dajin Soussan, inda ta hallaka fiye da ’yan ta’adda 100 a lokaci guda, lamarin da hukumomi suka bayyana a matsayin babbar nasara a yaƙin da ake yi da ta’addanci.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Rundunar Sojin Mali (FAMa) ta ce harin ya gudana ne a ranar Lahadi yayin aikin leƙen asiri da sa ido ta sama, inda jiragen yaƙi suka kai farmaki kan sansanin ’yan bindiga a yankin da ke yammacin Dioila da kudu maso yammacin Zantiguila. Rundunar ta ce ba wai kawai an kashe ’yan ta’adda sama da 100 ba, har ma an lalata makamai da motocin yaƙi masu yawa.
Mali na fama da rikicin tsaro tun daga shekarar 2012, musamman a yankunan arewa da tsakiyar ƙasar. A ’yan watannin nan, ƙungiyoyin ’yan ta’adda sun ƙara tsananta hare-hare bayan da gwamnati ta hana sayar da mai a wajen gidajen mai na hukuma, domin katse hanyoyin da suke samun fetur da sauran kayayyaki.














