Najeriya

Sarkin Ondo Mai Shekaru 22 Ya Gargadi Jama’a: Kada A Kira Shi “Bro” Ko “Blood”

Fadar Okeluse ta gargadi jama’a da su daina kiran Sarkin mai shekaru 22 da “bro” ko “blood”, tana mai cewa dole ne a rika kiran sa da Mai Martaba kawai, domin kare martabar sarauta da al’adar Yarbawa.

Newstimehub

Newstimehub

23 Jan, 2026

e034a1d1 2b3a 4cb0 af69 64fec6aaa54c 579x400 1

Fadar Arujale-Ojime na Masarautar Okeluse a Jihar Ondo ta fitar da gargaɗi mai tsanani ga jama’a kan amfani da kalmomin raini wajen kiran Sarkin, Oba Oloyede Adekoya Akinghare II, mai shekaru 22. Fadar ta bayyana cewa kiran Sarkin da sunaye irin su “bro” ko “blood” abin raini ne ga al’ada da martabar sarauta.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan Fada, Yarima Adefemi Olorunfemi, ya fitar, ya jaddada cewa dole ne a rika kiran Sarkin da Mai Martaba (His Royal Majesty) kawai. Ya ce duk wanda ya kauce wa wannan tsarin ba za a ƙara lamunta ba.

Yariman ya bayyana cewa wasu mutane na amfani da kalmomin zamani da sunan sabawa, amma a zahiri suna nuna rashin girmamawa. Fadar ta ce Sarkin wakilin alloli ne a doron ƙasa, kuma kursiyin da yake kai tsarki ne, don haka girmama shi na nufin girmama al’adar Yarbawa da tarihinsu.

An kuma tuna cewa Oba Akinghare ya hau karagar mulki tun yana ɗan shekara 16, bayan rasuwar mahaifinsa, kuma gwamnati ta amince da zaɓen sarakunan gargajiya bisa al’adar garin Okeluse.

Majiyar Labari: TVC NEWS