18 Jul, 2026

An kashe gomman sojojin ƙasar Mali a harin kwanton-ɓauna

‘Yan a-ware na ƙabilar Abzinawa a ƙasar Mali sun yi wa wani ayarin sojojin ƙasar kwanton-ɓauna a kusa da Anefis, kwanaki kaɗan bayan sojoji sun sake ƙwace garin na yankin arewa da ke da muhimmanci.

a5260364 6eb9 4eae 8dca 63dd9ed64165 1784386345917

18 Jul, 2026

Adadin ɗaliban da suka mutu a hatsarin motar Uganda ya kai 23

Bas ɗin na kan hanyarta ta dawowa babban birnin ƙasar, Kampala, daga wata tafiya ta makaranta zuwa wajen faɗuwar ruwa na Sipi Falls a gabashin Uganda ranar Alhamisa lokacin da motar da kauce daga kan hanya.

f6405f02 6bdf 422f a07b 25da64343a54 1784301692156

16 Jul, 2026

Uganda za ta sallami majinyacin Ebola na ƙarshe

Za a iya ayyana ƙasar a matsayin wadda ba ta da Ebola idan ba a samu sabbin rahotanni na mutanen suka kamu da cutar ba a cikin kwanaki 42 na sa idon Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

93aaec42 26f1 419c 8e81 77b1dd9014d8 1784185891643

13 Jul, 2026

Gwamnatin Mali ta tabbatar da kashe sojoji 30 a wani harin ta’addanci a arewacin ƙasar

Babban hafsan sojin Mali ya ce an kashe sojoji kusan 30 a fafatawar da aka yi kwanan nan don sake kwace babban garin Anefis da ke yankin arewacin ƙasar daga hannun ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyar Al Qaeda da kuma ‘yan awaren Tuareg.

cf1b3974 6276 4e42 a303 41b03d4cc5a3 1778259502930

10 Jul, 2026

Aikin matatar man Dangote zai ci gaba a gaɓar tekun Kenya, a cewar Shugaba Ruto

Shugaba William Ruto ya ce aikin wanda attajirin Nijeriya Aliko Dangote ke mara wa baya zai samar da ayyukan yi 60,000 tare da samar da mai a ƙasashen Afirka 8.

f7b3203e 473f 44d8 ad65 7031c28d6d8f 1780596631023

10 Jul, 2026

Afirka ta sami tallafin $900m domin faɗaɗa fasahar girki na zamani mara gurɓata muhalli

Tallafin ya fito ne daga haɗakar gwamnatocin duniya, masu zuba jari na kamfanoni masu zaman kansu, da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa masu fafutukar raya ƙasa.

bb9bee72 078d 4105 82bf 1226e52d12e0 1783665982745

9 Jul, 2026

‘Yansandan Afirka Ta Kudu sun ce mutuwar ɗan Nijeriya ba ta da alaƙa da tashin hankalin ci-rani

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan ya ce wata tawagar rundunar da ke bincike kan miyagun ƙwayoyi ta kama wani ɗan Nijeriya a gidansa a wani samame bisa bayanan sirri.

south africa corruption 93207 main

8 Jul, 2026

Sojojin Sudan sun ƙwace ƙauyen Al-Kurmuk bayan arangama da dama da RSF

Al-Kurmuk yana da muhimmanci sosai wajen sarrafa hanyoyin safarar kayayyakin soji da hanyoyin da suka haɗa Ethiopia ko Habasha da Sudan ta Kudu.

5eac08198a8ad4bd4f0f5c20527ac26c7c7baa0f657d5bd7c8721f97559d8b00

8 Jul, 2026

Rasha na son ƙarfafa alaƙa da Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) – Lavrov

“Muna da fahimta iri ɗaya kan buƙatar gina tsarin duniya na adalci mai rassa da yawa, da kuma haɗin gwiwarmu wajen yaƙi da dabarun sabon mulkin mallaka, waɗanda har yanzu suke tare da ƙawayenmu na Yammacin duniya,” in ji Lavrov.

68ca8788f356c2c8da0a290bce21820ad84cea7bf2a36d41dbac3dddc6e8d593 main

8 Jul, 2026

Jami’an tsaro a Afirka ta Kudu sun kama masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba fiye da 200

Ana zargin mutanen da hannu a hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a ƙasar, kamar yadda rundunar ‘yansandan ta bayyana a wani babban aikin haɗin gwiwa da sojoji kan yaƙi da laifuka.

2026 04 01t113010z 928342401 rc28gkaj4s5z rtrmadp 3 safrica politics army
Ana lodawa...